Yaki da ta’addanci: Gwamnatin Amurka ta sanar da antaya ma Najeriya dala miliyan 102

Yaki da ta’addanci: Gwamnatin Amurka ta sanar da antaya ma Najeriya dala miliyan 102

Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da baiwa Najeriya tallafi makudan kudi har dala miliyan 102, kimanin naira biliyan 3.9 kenan, da nufin tallafa ma kasar a kokarin da take yi na share hawayen mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito gwmanatin Amurka tace za’a yi amfani da kudin ne wajen samar ma yan gudun hijira wurin zama, abinci, magunguna da kuma samar musu da ingantaccen tsaro.

KU KARANTA: Uba, Uwa, Yara 3 da abokinsu 1 sun yi mutuwar ban mamaki kwana daya da tarewa a sabon gida

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sanarwar na cewa: “rikicin Boko Haram da aka kwashe kusan shekaro 10 ana fama da shi ya sabbaba matsaloli da dama ga mutane, wanda yayi sanadin mutuwar mutum miliyan biyu, yayin da wasu miliyan 11 ke cikin mawuyacin hali

Yaki da ta’addanci: Gwamnatin Amurka ta sanar da antaya ma Najeriya dala miliyan 102

Sansani

“Muna sa ran yin amfani da kudin wajen samar wurin zama, abinci, magunguna, tsaftataccen ruwan sha ga yan gudun hijira tare da baiwa mata da aka yi ma fyade kulawa, da kuma marayu, haka zalika muna fata masu ruwa da tsaki zasu lalubo hanyar dawo da zaman lafiya a yankin.” Inji su.

Wani bincike ya nuna cewara watan Mayu shekarar 2018, akwai mutane miliyan 2.3 dake halin tsananin bukatar abinci, tsaro, bugu da kari a gaba daya yankin Arewa maso gabas akwai mutane miliyan 7.7 dake bukatar agaji.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel