Likafa ta ci gaba: Majalisar Dinkin Duniya ta sake baiwa yar Najeriya babban mukami

Likafa ta ci gaba: Majalisar Dinkin Duniya ta sake baiwa yar Najeriya babban mukami

Kimanin shekara daya kenan da majalisar dinkin Duniya ta zabi tsohuwar ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Amina Mohammed a matsayin mataimakiyar Sakataren majaliar dinkin Duniya, sai ga shi a yanzu an sake kwatawa, inda majalisar ta zabu wata zakakurar yar Najeriya.

Premium Times ta ruwaito Majalisar ta nada Uwargida Ahunna Eziakonwa a matsayin mataimakiyar Darktan na hukumar cigaban kasashen Duniya UNDP, reshen nahiyar Afirka.

KU KARANTA: Uba, Uwa, Yara 3 da abokinsu 1 sun yi mutuwar ban mamaki kwana daya da tarewa a sabon gida

Uwargida Ahunna zata maye gurbin tsohon mataimakin Darakta da ya fito daga kasar Sanigal Abdoulaye Mar Dieye, wanda ya samu karin girma zuwa babban daraktan UNDP.

Likafa ta ci gaba: Majalisar Dinkin Duniya ta sake baiwa yar Najeriya babban mukami

Ahunna

Sai dai dama can Ahunna ta rike mukamai daban daban a majalisar dinkin Duniya, inda a baya bayan nan itace wakiliyar majalisar a kasar Habasha, haka zalika kafin nan ma ta taba zama wakiliyar majalisar a kasar Uganda.

Daga karshe majiyar Legit.ng ta ruwaito Ahunna ta taba aiki da rundunar Sojojin majalisar dinkin Duniya dake kwantar da tarzoma, da wannan nadin nata, Ahunna ta zamo mace ta biyu yar Najeriya dake rike da wani muhimmin mukami a UN.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel