"Najeriya ka iya fadawa cikin matsanancin yaki idan majalisa ta tsige Buhari"

"Najeriya ka iya fadawa cikin matsanancin yaki idan majalisa ta tsige Buhari"

Daya daga cikin 'ya'yan majalisar dokoki a Najeriya mai suna Honorable Lawal Yahaya Gumau ya yi hasashen cewa barazanar tsige Shugaba Buhari da majalisar tarayya ke kokarin yi a matsayin wani abu da zai iya jawo yaki a zauren majalisar dokokin kasar.

Shi dai dan majalisar kamar yadda muka samu yana wakiltar karamar hukumar Toro ne ta jihar Bauchi dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan kuma ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ga wadansu 'yan majalisar da ke barazanar tsige Shugaba Buhari.

"Najeriya ka iya fadawa cikin matsanancin yaki idan majalisa ta tsige Buhari"

"Najeriya ka iya fadawa cikin matsanancin yaki idan majalisa ta tsige Buhari"

KU KARANTA: EFCC ta fitar da sabuwar muhimmiyar sanarwa

Legit.ng ta samu cewa dan majalisar ya kuma ce tsige shugaban ba abun da zai yiwu ba ne cikin ruwan sanyi, domin a cewarsa, "talakawa suna son shi kuma suna jin dadin manufofinsa."

A wani labarin kuma, Fitaccen mai kudin nan dan Najeriya kuma shugaban kamfanin da ke kera motoci a Najeriya na IVM Innoson watau Cif Innocent Chukwuma a ranar alhamis din da ta gabata ya ba wata kungiyar kamfe din Buhari na zaben 2019 kyautar motoci biyu.

Motocin dai wadanda dukkan su sabbi ne samfurin SUV IVM G5 da kuma bas din Innoson samfurin IVM 5000A an mika su ne ga kungiyar Muhammadu Buhari/ Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group da ke fafutukar ganin shugaba Buhari ya zarce a 2019.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel