Maboyar bama-bamai ta 'yan Shi'a a masallaci ta tarwatsa mutane 17

Maboyar bama-bamai ta 'yan Shi'a a masallaci ta tarwatsa mutane 17

Wasu abubuwan fashewa da ake kyautata zaton bama-bamai ne sun halaka mutane 17 tare da jikkata wasu mutanen 80 dake a wani masallaci a babban birnin kasar Iraki, in ji majiyoyin mu na lafiyar kasar.

Ita dai gwamnatin kasar kamar yadda muka samu ta bayyana cewa lamarin da ya auku a daren Laraba ya samu asali ne daga fashewar ma'ajiyar makamai a unguwar 'yan Shia da ke birnin Sadr.

Maboyar bama-bamai ta 'yan Shi'a a masallaci ta tarwatsa mutane 17

Maboyar bama-bamai ta 'yan Shi'a a masallaci ta tarwatsa mutane 17

KU KARANTA: Yarbawa sun ce a tsige Buhari

Legit.ng ta samu cewa gwamnatin ba ta bayar da bayanin ainihin inda ma'ajiyar makaman take ba, amma wasu jami'an tsaro a kasar sun ce a cikin wani masallaci ne da magoya bayan malamin Shi'ia Moqtada Al-Sadr su ne suke amfani da shi.

Sai dai hotunan da aka dauka bayan fashe-fashen sun nuna cewa fashewar makaman tayi kasa-kasa da masallacin tare da lalata gidajen da suke kusa da kuma wasu gine-ginen.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel