Da dumin sa: Sojoji sun yiwa mayakan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe 4 tare da kwato makamai (Hotuna)

Da dumin sa: Sojoji sun yiwa mayakan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe 4 tare da kwato makamai (Hotuna)

Dakarun hukumar sojin Najeriya runduna ta 192 dake aikin tabbatar da zaman lafiya karkashin atisayen ofireshon lafiya a jihar Borno, ta yiwa mayakan kungiyar Boko Haram kwanton bauna a kan hanyar kauyen Lokodisa dake karamar hukumar Gwoza.

Dakarun sojin sun yi nasarar yiwa mayakan kwanton baunar ne da safiyar yau, Alhamis, bayan samu bayanan sirri a kan motsin mayakan. Sojojin sun kasha mayakan kungiyar Boko Haram 4 tare da kwato wasu bindigu 3 da kekuna 5.

Da dumin sa: Sojoji sun yiwa mayakan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe 4 tare da kwato makamai (Hotuna)

Sojoji sun yiwa mayakan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe 4 tare da kwato makamai

Da dumin sa: Sojoji sun yiwa mayakan Boko Haram kwanton bauna, sun kashe 4 tare da kwato makamai (Hotuna)

Bindigun da aka kwato

A wata arangamar daban, rundunar soji ta 145 tayi nasarar kasha wani mayakin kungiyar ta Boko Haram a kauyen Gashigar dake karkashin karamar hukumar Abadam, a jihar ta Borno. An kasha shi ne a yayin da mayakan ke kokarin tserewa ta wata barauniyar hanya bayan fuskantar matsin lamba daga dakarun soji.

DUBA WANNAN: Fashin Offa: Duba hotunan shaidun da 'yan sanda ke tunkaho da su a kan Saraki

Kazalika an karbi wasu ‘yan gudun hijira kimanin su 38 a sansanin ‘yan gudun hijira dake Gamboru a karamar hukmar Ngala bayan dawowar su daga jamhuriyar Kamaru.

Daga cikin ‘yan gudun hijirar akwai maza 11, mata 6 da kananan yara 21. An damka su hannun jami’an dake kula da sansanin gudun hijira.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel