Iyalin Abiola sun yabawa abin da Shugaba Buhari yayi wa Mahaifin su

Iyalin Abiola sun yabawa abin da Shugaba Buhari yayi wa Mahaifin su

- Shugaban kasa Buhari ya karrama wanda ake tunani ya lashe zaben 1993

- Iyalin Marigayi M.K.O Abiola sun ji dadin wannan abu da Gwamnati tayi

- Wasu dai su na gani akwai makarkashiyar siyasa a matakin da aka dauka

Mun samu labari cewa Iyalan Marigayi Mashood Kashimawo Olawole Abiola sun ji dadin abin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi na girmama Mahaifin su da kuma tunawa da zaben shugaban kasa da aka soke na 1993.

Iyalin Abiola sun yabawa abin da Shugaba Buhari yayi wa Mahaifin su

Lokacin da Abiola yake kamfe a karkashin Jam'iyyar SDP a 1993

‘Daya daga cikin Yaran da Marigayin ya bari ta bayyana farin cikin ta a shafin ta na Tuwita. Wura Abiola ta dauki lokaci ya godewa Shugaban Kasa Buhari da ya karrama Marigayi Abiola da lambar GCFR da sai shugaban kasa ake ba a Najeriya.

KU KARANTA: Wani Soja ya nuna jaruntaka a gaban wasu 'Yan fashi

Ita ma Rinsola Abiola wanda ‘Diyar Marigayin ce kuma tana cikin manya a Jam’iyyar APC mai mulki tace Shugaban Kasa Buhari yayi abin a-yaba masa ko da wasu na kokarin alakanta matakin da Gwamnatin Buhari ta dauka da siyasar 2019.

Sauran Jama’a da su kayi gwagwarmaya a wancan lokaci dai sun ji dadin karrama Mashood Abiola da aka yi bayan rayuwar sa. Ba shakka M.K.O Abiola ne ya lashe zaben 1993 da Shugaban Kasa na mulkin Soja a lokacin Janar Ibrahim Babangida ya soke.

Babban 'Dan Mariagayi Abiola watau Mista Kola Abiola ya aika sakon godiya da farin ciki ga Shugaban Kasa Buhari na daukar wannan mataki. Yanzu haka dai Kola Abiola ba ya Kasar amma ya aiko takarda jiya da yamma kamar yadda labari ya zo mana.

Yanzu dai Gwamnatin Tarayya ta maida ranar Damukaradiyya zuwa 12 ga watan Yuni a maimakon 29 ga Watan Mayu da aka saba. Bayan nan kuma Shugaban Kasa Buhari ya karrama Babagana Kingibe da kuma babban Lauyan kasar Marigayi Gani Fawehimi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel