Reshe ya juye da mujiya wajen zaben shugabanni na Jam’iyyar APC

Reshe ya juye da mujiya wajen zaben shugabanni na Jam’iyyar APC

- Wasu na hannun daman Shugaban kasa Buhari sun sha kashi a zaben APC

- APC tayi watsi da yaron Tinubu da aka zaba a matsayin Shugaban Jam’iyya

- A Jihar Kwara mai dai Bukola Saraki ya goge raini da Ministan yada labarai

Mun samu labari cewa wasu da ke kokarin rike madafan iko na Jam’iyyar APC mai mulki a Jihohin Kasar nan ba su samu yadda su ka so ba. Sai dai kuma wasu manya a APC sun ji dadin yadda abubuwa su ka kaya kwanan nan. Tinubu yana cikin wadanda su ka sha kasa.

Reshe ya juye da mujiya wajen zaben shugabanni na Jam’iyyar APC

Jam'iyyar APC ta rantsar da Balogun a maimakon Oke a Legas

A Jihar Ribas mun fahimci cewa Sanatan Jihar Magnus Abe bai ji dadin yadda zaben Shugabannin Jam’iyyar ya kasance ba ganin Ojukate Amachree ne ya zama Shugaban Jam’iyya a Jihar. Amachree dai yana tare ne da tsohon Gwamnan Jihar Rotimi Amaechi.

KU KARANTA: PDP ta fallasa wasu kudi da aka wawure a Gwamnatin Buhari

A Jihar Oyo kuma Ministan sadarwa Adebayor Shitu bai ji dadin yadda abin ya kasance va. Akin Oke wanda aka zaba kuma aka rantsar a matsayin Shugaban APC yana tare ne da Gwamnan Jihar Abiola Ajimobi. Shittu yana harin kujerar Gwamnan Jihar Oyo a 2023.

Kamar yadda mu ka ji a Jihar Imo dai Gwamna da kan sa ne ya sha kasa inda yayi kokarin kakaba yaran sa a kan kujerun shugabannin Jam’iyyar. Hakan dai bai yiwu ba inda har ta kai Gwamna Rochas Okorocha yace sai ya sa an daure Shugabannin APC na kasa.

A Jihar Kwara Bukola Saraki ya nunawa Ministan labarai Lai Mohammed cewa har yanzu shi yake da ta cewa a APC inda Masood Bolarinwa ya zama Shugaba a Jihar. A Legas dai Tunde Balogun wanda ba ya tare da Bola Tinubu aka rantsar a matsayin Shugaban APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel