Kotu ta aikewa da El-Rufa'i kashedi na karshe a kan kin biyayya ga umarnin ta

Kotu ta aikewa da El-Rufa'i kashedi na karshe a kan kin biyayya ga umarnin ta

Wata babbar kotu dake zaman ta a Kaduna ta aikewa da gwamna El-Rufa’i wata takardar kashedin kin yin biyayya ga umarnin ta. Kotun ta aike da takardar ne ta hannun ofishin sakataren gwamnati da kuma hukumar tattara haraji da raya jihar Kaduna(KADIRS).

Kotun ta aike da takardar ne a matsayin tuni ga takardar umarnin dakatar da gwamnatin jihar Kaduna daga rushe gidan Sanata Suleiman Hunkuyi.

A ranar 28 ga watan Mayu ne hukumar KADIRS ta aikewa Sanata Hunkuyi takardar tunin neman ya biya miliyan N31m na filin gidansa da ya gina duk da kotu ta dakatar da gwamnatin jihar daga daukan wani mataki a kan batun rushe gidan Sanatan.

Kotu ta aikewa da El-Rufa'i kashedi na karshe a kan kin biyayya ga umarnin ta

El-Rufa'i da Sanata Hunkuyi

A ranar 6 ga watan maris ne kotun ta bayar da bayar da umarnin dakatar da gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin ta daga taba gidan Sanata Hunkuyi dake fili mai lamba 18A a kan titin Inuwa Wada dake unguwar Rimi a garin Kaduna.

DUBA WANNAN: PDP ta bawa APC a zaben maye gurbi na karamar hukumar Jaba a jihar Kaduna

Tunda farko, Sanata Hunkuyi ne ya garzaya kotun domin neman ta dakatar da gwamnatin jihar daga yunkurin tan a rushe masa gidan sa bayan ta rushe wani gidan nasa da ya bayar ga jam’iyyar APC.

Saidai gwamnatin jihar tayi burus da umarnin kotun tare da sake aikewa Sanata Hunkuyi takardar tunin cewa zata rushe gidan sa muddin bai hanzarta biyan harajin miliyan N31m ga gwamnati ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel