Amurka ta sake bayar da tallafi mai tsoka ga wadanda ta’annatin ‘yan Boko Haram ya shafa

Amurka ta sake bayar da tallafi mai tsoka ga wadanda ta’annatin ‘yan Boko Haram ya shafa

- Anyi wa Najeriya alkawarin sake tallafa mata da Dala Miliyan $102m domin agazawa wadanda yakin Boko Haram ya daidaita

- Amma sai dai wakilan kungiyar gamayyar Turai sun yi kira da a samu hadin kai mai karfi tsakanin jami'an tsaro

Jakadan Gwamnatin kasar Amurka a Najeriya Mr Stuart Symington a yau Alhamis ya shaida cewa kasarsa zata sake bayar da wasu karin dala miliyan $102m domin tallafawa wadanda rikicin ‘yan Boko Haram ya rutsa da su a Arewa maso Gabas.

Amurka ta sake bayar da tallafi mai tsoka ga wadanda ta’annatin ‘yan Boko Haram ya shafa

Amurka ta sake bayar da tallafi mai tsoka ga wadanda ta’annatin ‘yan Boko Haram ya shafa

Stuart Symington ya shaida wannan batu ne yayin wata tattaunawa akan sha’anin bayar da tallafi don cigaban rayuwar ‘dan Adam a Abuja.

Inda yayi jawabin cewa kudaden za’ayi amfani da su ne wajen habaka bangaren abinci da matsugunnai da fannin lafiya da kuma sha’anin tsaro ga dunbin wadanda rikicin ya rutsa da su.

Kuma tallafin zai kasance ne karkashin kulawar cibiyar bayar da taimako ga kasashen waje ta Amurka (USAID) da sashin lura da abinci da kuma tabbatar da zaman lafiya (FFP) tare da Ofishin mai lura da agaji kan annoba da iftila’i (OFDA) da kuma sashin kididdigar al’umma da ‘yan gudun hijira da kuma bakin haure na Ofishin kasa da kasa.

KU KARANTA: Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun 'dan fashi da makami

Fatan Mu shi ne wannan tallafi na habaka rayuwar al’umma da muka bayar da kuma kokarinda Gwamnatin Najeriya take yi ya taimaka wurin samar da zaman lafiya da karuwar arziki.” Jakadan ya bayyana.

Symington ya kuma ce kididdiga ta nuna a watan Mayun da ya gabata akwai mutane miliyan 2.3m a yankin Arewa maso yamma da suke cikin matsanancin rashin abinci.

Kuma a cewarsa hakan baya rasa nasaba da yawaitar rashin tsaro da ya tilastawa Mutane da yawan gaske yin kaura daga muhallinsu alhali yawancinsu manoma ne.

Hashe kuma ya nuna cewa Mutane miliyan 7.7m ne a yankin na Arewa maso yamma ke mutukar bukatar tallafi domin sasaita rayuwarsu.

Amurka ta sake bayar da tallafi mai tsoka ga wadanda ta’annatin ‘yan Boko Haram ya shafa

Amurka ta sake bayar da tallafi mai tsoka ga wadanda ta’annatin ‘yan Boko Haram ya shafa

“Duk kuwa da cewa Sojojin Najeriya sun samu nasarar mayarwa da wasu gonakinsu da yawa daga cikin wadanda yakin ya daidaita”.

“Gwamnatin Amurka ita ce wadda tafi kowacce kasa bayar da tallafi ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a yankin tafkin Chadi, inda ta bayar da taimakon sama da $761m tun shekarar 2017:” Symington ya jaddada.

Haka zalika a yayin taron, wakilan kungiyar gamayyar kasashen turai Mr Richard Young, kira yayi ga hukumomin tsaro da su tabbatar da an cigaba da samun hadin kai a tsakaninsu domin hakan zai taimaka wajen bayar da agaji ga Mutane yadda ya kamata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel