Gwamnatin Tarayya za ta rabawa Talakawan Najeriya motocin cikin sauki

Gwamnatin Tarayya za ta rabawa Talakawan Najeriya motocin cikin sauki

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hada kai da babban bankin Afrika watau AfdB domin ganin an kera wasu motoci da za a saida su a kan kudi N200, 000 kacal.

A wajen wani taro da bankin AfdB na cigaban Nahiyar Afrika ta shirya da Ma’aikatar kwadago mun ji cewa Najeriya za ta hada karfi da karfe da bankin na AfDb domin ganin an raba wasu motoci kirar Peugeot cikin farashi mai rahusa a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya za ta rabawa Talakawan Najeriya motocin cikin sauki

Shugaban babban bankin cigaban Afrika Akinwumi Adesina

Ebirima Faal wani babban Darektan bankin na AfdB a Afrika yake cewa za a samar da wadannan motoci masu nagarta na Peugeot har 400 wandaza a saida su a kan kudi N200, 000 ba tare da karbar wani jingina ko biyan wani karin kudi can daga baya ba.

KU KARANTA: Saraki ya bayyana abubuwan da ake sa ran Buhari yayi

Ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige dai ya tabbatar da wannan yarjejeniya da bakin sa inda yace za a rabawa wadannan motoci ne ga ‘yan kasar. Matakin da za a bi wajen saida motocin dai shi ne la’akari da wanda ya fara tayawa inji Ministan Kasar.

Gwamnatin Najeriya ta yabawa Shugaban bankin AfdB da wannan kokari ta kuma bada adireshin da masu bukatar wadannan motoci za su aika takardar su. Hakan dai zai ba Talaka dama shi ma ya mallaki zukekiyar mota cikin farashi mai sauki a Najeriya.

Kwanaki kun ji cewa Kamfanin Dangote zai samu damar kere-kere da kuma hada motocin Peugeot a Garin Kaduna. An shiga yarjejeniya ne tsakanin Kamfanin Peugeot da da Aliko Dangote kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel