Yanzu Yanzu: majalisar dattawa ta ki amincewa da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar rantsar da sabbin jami’an gwamnati

Yanzu Yanzu: majalisar dattawa ta ki amincewa da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar rantsar da sabbin jami’an gwamnati

A ranar Alhamis, 7 ga watan Yuni, majalisar dattawa ta yi watsi da June 12 a matsayin ranar kaddamar da sabbin jami’an gwamnati.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar a shafinsa na Facebook cewa June 12 zai koma ranar damokradiyya.

Majalisar masu rinjayen tace lallai ranar 29 ga watan Mayu shine ranar rantsar da sabbin jami’an kasar.

Yanzu Yanzu: majalisar dattawa ta ki amincewa da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar rantsar da sabbin jami’an gwamnati

Yanzu Yanzu: majalisar dattawa ta ki amincewa da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar rantsar da sabbin jami’an gwamnati

Yan majalisan sun kuma bayyana bukatar biyan dukkanin kudaden albashi da alawus alawus din manyan jami’an da aka zaba a waccan lokacin ga iyalansu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro karo na 3 a mako daya

A halin da ake ciki, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya bayyana cewa akwai bukatar gyara kundin tsarin mulki idan har 12 ga watan Yuni ya koma ranar Demokradiyya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel