Da dumin sa: Kotu ta goyi bayan sifeton ‘yan sanda, ta bashi ikon daukan mataki a kan Saraki

Da dumin sa: Kotu ta goyi bayan sifeton ‘yan sanda, ta bashi ikon daukan mataki a kan Saraki

- Shugaban runndunar ‘yan sanda(IGP), Ibrahim Idris, ya samu sahalewar kotu na daukan matakin shari’a a kan majalisar dattijai da shugan ta, Bukola Saraki

- Idris ya maka Saraki da majalisar dattijai a kotu bisa ayyana shi a matsayin makiyin dimokradiyya da bai kamata ya rike wani mukami na mulkin jama’a ba

- Alkalin wata babbar kotun tarayya dake Abuja,John Tsoho,ya bawa IG Idris wannan dammar

Ibrahim Idris, babban sifeton rundunar ‘yan sanda na kasa yam aka majalisar dattijai da shugaban ta, Bukola Saraki, gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja bisa bayyana shi a matsayin makiyin dimokradiyya da bai dace da rike wani ofishi na shugabancin jama’a ba da majalisar ta yi.

Da dumin sa: Kotu ta goyi bayan sifeton ‘yan sanda, ta bashi ikon daukan mataki a kan Saraki

Saraki da IGP Idris

A yau ne, Alhamis, 7 ga watan Yuni, Idris ya sami sahalewar babbar kotun karkashin mai shari’a, John Tsoho, domin shigar da karar majalisar da kuma Bukola Saraki domin fara sauraro a gaban ta.

DUBA WANNAN: Wata kalma cikin wasikar Buhari ta saka sanatoci kyalkyalewa da dariya

A ranar 9 watan Mayu ne majalisar dattijai ta bayyana cewar IG Idris bai dace ya zama jagoran jama’a ba saboda makiyin siyasa ne. Majalisar ta bayyana hakan ne bayan IG Idris ya ki amsa gayyatar da tayi masa a karo na uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel