Badakalar fashin Offa: Hotunan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

Badakalar fashin Offa: Hotunan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

A cigaba da badakalar fashin garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu da hukmar ‘yan sanda ke bincike, hukumar ta saki wasu hotuna da t ace ta ci karo da su ne yayin binciken da take gudanarwa.

A ranar Talata ne, hukumar ‘yan sanda ta fitar da cikakken jawabin shugaban ‘yan fashin da ake kira AY inda ya bayyana cewar su yaran Saraki ne.

Badakalar fashin Offa: Hotunan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

Abubuwan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

Badakalar fashin Offa: Hotunan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

Hotunan abubuwan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

AY, shugaban ‘yan fashin da kuma wata kungiya Liberation Youth Movement dake kudancin jihar ya shaidawa ‘yan sandan cewar, “muna da alaka da shugaban majalisar dattijai domin mu yaran sa ne. Muna nan a kowanne bangare na jihar Kwara kuma mun dade muna yi masa aiki tun yana jam’iyyar PDP.”

DUBA WANNAN: PDP ta rangada APC da kasa a zaben maye gurbi a jihar Kaduna

Da hukumar ‘yan sanda ta tambaye shi ko wane irin aiki suke yiwa Saraki, sai AY y ace, “mune ke yi masa bangar siyasa musamman a wuraren da muka ga alamun ba zamu samu nasarar zabe ba.

Badakalar fashin Offa: Hotunan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

'Yan fashin Offa

Badakalar fashin Offa: Hotunan da binciken hukumar ‘yan sanda ya gano

Motar 'yan fashin Offa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel