Rashin kai zuciya nesa ya sanya wani Saurayi kashe ‘dan uwansa akan Komfuta Laptop

Rashin kai zuciya nesa ya sanya wani Saurayi kashe ‘dan uwansa akan Komfuta Laptop

- Wani saurayi ya cika wandonsa da iska sakamakon zuciya da ta debe ya kashe ‘dan uwansa

- Kisan ya biyo bayan bacewar kwamfutarsa da ya zargin ‘dan uwannasa Ifeanyi Ibeawuchu mai shekaru 22

- Wannan abin tsautsayin dai ya faru ne a yankin Umudagu dake garin Mbieri na jihar Imo

Jaridar Punch ta rawaito cewa ‘dan uwan wanda aka kashen Uchechukwu ya samu labari ranar Lahadi 3 ga watan Yuni wani mai suna Ibeawuchi ya tuhumi mamacin da daukar masa kwamfutarsa ta Laptop amma shi kuma mamacin ya musanta zargin.

Rashin kai zuciya nesa ya sanya wani Saurayi kashe ‘dan uwansa akan Komfuta Laptop

Rashin kai zuciya nesa ya sanya wani Saurayi kashe ‘dan uwansa akan Komfuta Laptop

Sai dai duk da haka Ibeawuchi ya ki kyale shi, daga bisani yazo da wasu mutane 3 a matsayin ‘yan sanda suka tafi da shi Ogu.

Uchechukwu ya kuma kara da cewa a ranar 5 ga watan Yuni ne ya samu labarin an kashe masa ‘dan uwansa kuma gawar ma tana sashin ajiye gawawwaki na babban asibitin Umuguma.

“Na ziyarci Ofishin ‘yan sanda amma sai suka fada min cewa kanina baya Ofishin nasu. Amma koda muka sami gawarsa a asibiti sai suka fada mana cewa ai Ibeawuchi ne ya kawo gawar tasa”.

KU KARANTA: An kama sojan bogi dauke da katin shaidan jami'in 'dan sanda

Mahaifi ga mamacin Nathel Ogu ya dage cewa lallai sai gaskiya tayi halinta ba zai yafe ba, amma sai dai a ranar Laraba 6 ga watan Yuni wasu fusatattun matasa suka dauki doka a hannunsu ta hanyar kona wani gidan dangin wanda yayi kisan.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ta Imo SP Andrew Enwerem ya bayyana cewa yanzu haka sun samu nasarar dawo da zaman lafiya a yankin, kuma sun fara binciken yadda abin ya faru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel