Kotu ta ba Dino Melaye hutu don ya tafi kasar waje yin magani

Kotu ta ba Dino Melaye hutu don ya tafi kasar waje yin magani

Wata babbar kotun majistare dake Wuse, Abuja ta ba Sanata Dino Melaye (APC, Kogi) hutu domin ya tafi kasar Amurka ganin likitansa.

An gurfanar da Melaye a gaban kotu a ranar 2 ga watan Mayu kan zargin sa da yunkurin tserewa daga wani motan yan sanda a Abuja a ranar 24 ga watan Afrilu.

Da aka dawo zaman kotu a jiya, lauyansa, John Odubela (SAN) ya roki kotu da ta umurci kwamishinan yan sanda, na tarayya day a saki fasfot din Melaye domin ya samu damar fita waje domin ganin likita.

Kotu ta ba Dino Melaye hutu don ya tafi kasar waje yin magani

Kotu ta ba Dino Melaye hutu don ya tafi kasar waje yin magani

Odubela ya fadama kotu cewa Melaye nada cutar asthma sannan kuma cewa lafiyarsa ya samu tangarda. Yace kuma Melaye na da ganin likita a ranar 28 ga watan Yuni a Amurka.

KU KARANTA KUMA: A nuna mani aiki 1 da Buhari ya kammala a shekaru uku — Tanko Yakasai

Da take yanke hukunci, shugabar kotun, Mabel Segun-Bello tace tunda dai halin rashin lafiyan na tattare da shi kafin shari’an sannan kuma yana da ganin likita a kasar waje, babu wani bukatan wasika daga gare su.

Ta ba da umurnin a sake masa fasfot dinsa sannan kuma cewa ya kasance a wajen kasar ne na tsawon kwanaki 20 (Yuni 18 zuwa Yuli 8). An kuma umarce shi da ya dawo da fasfot din ga kwamishinan yan sanda da zaran ya dawo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel