Majalisar dattawa ta warware amincewa da nadin wani kwamishinan zabe saboda wani dalili

Majalisar dattawa ta warware amincewa da nadin wani kwamishinan zabe saboda wani dalili

Majalisar dattawa ta sanar da janye amincewar da tayi wa Monday Udo Tom a matsayinsa na baturen zabe na jihar Akwa Ibom.

An dai tantance Tom ne a ranar Laraba tare da wasu mutane uku da aka amince ta tabbatar da su a matsayin turawan zabe.

Sai dai a yau Alhamis, Majalisar dattawan da janye amincewar da tayi wa Tom bayan Sanata Akpan Bassey mai wakiltan arewa maso kudancin Akwa Ibom ya janyo gabatar da kudirin janye amincewar.

Bassey ya ce kwamitin majalisar dattawa a kan hukumar zabe mai zaman kanta INEC ba ta sanya wani rahoton korafi da aka rubuta game da Tom ba.

Majalisa ta janye amincewar da tayi wa wani kwamishinan INEC

Majalisa ta janye amincewar da tayi wa wani kwamishinan INEC

KU KARANTA: PDP ta sha kaye a hannun APC a zaben ciyaman na karamar hukumar Chikun a Kaduna

"Ina son in jawo hankalin majalisar a kan batun tantane Udo Tom wanda shine aka zaba a matsayin baturen zabe na jihar Akwa Ibom," inji shi.

"Zanyi amfani da wannan damar don janyo hankalin kwamitin INEC karkashin jagirancin Nazif da cewa ni da kwamitin mun samu rubutaciyar korafi a kan Tom a ranar 5 ga watan Fabrairun 2018 amma rahoton kwamitin da aka gabatar wa majalisa baya dauke da wannan korafin.

"A hannu na akwai rahoton kwamitin a shafi na biyar kuma banga an ambaci korafin ba duk da cewa an aike wa kwamitin da'a da sauraron koke-koken al'umma takardan korafin."

Hakan yasa Sanata Akpan ya bukaci mahukuntan majalisar sun janye amincewar da akayi wa Tom har sai lokacin da majalisar da karasa gudanar da bincike a kan korafinsa sannan a san matakin da za'a dauka.

Bayan an tabatar da cewa takardan korafin ya ishe gaban kwamitocin majalisar, Shugaban majalisa Bukola Saraki ya tabbatar da janyewar amincewar da majalisa ta yi wa Tom kuma ya mika batun ga kwamitin INEC don sake bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel