Babbar annoba ta dawo: Kyandar Biri ta bulla a jihar Plateau

Babbar annoba ta dawo: Kyandar Biri ta bulla a jihar Plateau

- Wata Cuta da akai murnar tafiyarta ta sake dawowa

- Kwamishinan lafiya na jihar Plateau ne ya shaidawa manema labarai yau Alhamis

- Sannan ya lissafo wasu abubuwa da ya kamata a gujewa domin yin hannun riga da Cutar

Gwamnatin jihar Plateau ta tabbatar da kamuwar wasu Mutane biyu da mummunar cutar nan ta Kyandar Biri a yankin karamar hukumar Shendam ta jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Kunden Deyin ne ya shaida hakan yayin da yake tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), cewa wannan shi ne karon farko da aka samu tabbacin bullar cutar a jihar.

Babbar annoba ta dawo: Kyandar Biri ta bulla a jihar Plateau

Babbar annoba ta dawo: Kyandar Biri ta bulla a jihar Plateau

Kwamishinan ya shaidawa NAN faruwar wannan lamari ne yau Alhamis a garin Jos. Ya ce an samu cutar a jikin wasu Mutane biyu da suka zo daga birnin Fatakwal na jihar Rivers domin neman magani.

Deyin ya ce da farko dai daya ne ya fara kamuwa kafin daga bisani ya shafawa gudan, dukkanninsu dai an basu magani a asibitin koyarwa na Bingham. Kuma yanzu haka cibiyar dakile manyan cutuka masu hadari ta jihar na cika da bincike don kiyaye yaduwar cutar.

KU KARANTA: Sabuwar ranar Dimukuradiyya: Su wa da wa ya kamata ku san rawar da suka taka a zaben 12 ga watan Yuni 1993

Kwamishinan ya kuma kara da cewa alamomin cutar Kyandar Birin iri daya ne da na cutar Kyanda amma sai dai nata tafi tsanani. Sai dai ya bayyana cewa asali cutar a jikin dabbobi ake daukarta kafin daga bisani idan Mutum ya kamu ya gogawa dan uwansa Mutum idan sun yi cudanya.

A don haka ne Deyin ya gargadi masu farautar dabbobin daji kamar Bera, Dage, Kurege da kuma Birrai da dai sauransu, domin masu ta'ammali da su na cikin hadarin kamuwa da kwayar cutar.

Sannan ya bukaci jama’a da su kai rahotan bullar cutar amai da gudawa da duk wata irin cuta da ta feso a ciki da basu gane ko wacce ba ce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel