Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro karo na 3 a mako daya

Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro karo na 3 a mako daya

A ranar Alhamis, 7 ga watan Yuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin tsaro da na sauran hukumomin tsaro a ofishinsa dake fadar shugaban kasa.

Ganawar ita ce ta uku a cikin mako daya. Hakan na zuwa ne lokacin da lamarin tsaro suka tabarbare a wasun yankunan kasar musamman a jihohi irinsu, Benue, Taraba, Kaduna da Zamfara.

An fara ganawar ne da misalin 2:30pm. Ya samu halartan dukkanin shugabannin hukumomin tsaro ciki harda babban darakta na hukumar liken asiri na kasa (NIA), Ahmed Abubakar.

Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro karo na 3 a mako daya

Yanzu Yanzu: Buhari ya sake ganawa da shugabannin tsaro karo na 3 a mako daya

An kawo karshen ganawar da karfe 3:00pm.

KU KARANTA KUMA: A nuna mani aiki 1 da Buhari ya kammala a shekaru uku — Tanko Yakasai

Babu wanda ya yarda yayi Magana da yan jarida cikinsu akan abunda ganawar ya kunsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel