Gwamna Al-Makura ya yafewa Fursunoni 35, ya Biya Tarar Mutane 28 a jihar Nasarawa

Gwamna Al-Makura ya yafewa Fursunoni 35, ya Biya Tarar Mutane 28 a jihar Nasarawa

Wani sabon rahoto da muka samu da sanadin wallafa ta shafin jaridar Daily Trust ya bayyana yadda Gwamna Tanko Al-Makura ya sayawa kansa Rigar Mutunci mai tsadar gaske cikin jihar sa a wannan wata mai Albarka na Ramadana.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura, ya yafewa wasu Fursoni 35 tare da sauke nauyin tarar da ke kan wasu mutane 28 a jihar sa.

Lauyan Kolu kuma Kwashinan Shari'a na jihar, Abdulkarim Kana, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da Manema Labarai a Babban Birnin Jihar na Lafia.

A sanarwar da Kwamishin ya bayar a ranar Alhamis ta yau, ya bayyana cewa gwamnan ya yafewa Fursunonin ne a sanadiyar tanadi da sashe na 212 da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya gindaya.

Kana yake cewa, gwamnan ya yanke wannan hukunci ne a sanadiyar daukan shawara da Majalisar Jin Kai ta Jihar ta bayar, inda ya yafewa Fursunoni 35 a jihar sa.

Gwamnan jihar Nasarawa; Umaru Tanko Al-Makura

Gwamnan jihar Nasarawa; Umaru Tanko Al-Makura

Ya ci gaba da cewa, Gwamnan ya kuma sauke nauyin tarar dake kan wasu mutane 28 da su ka gaza biya yayin da kotu ta ba su zabin biya dangane da rashin girman laifukan da suka aikata.

KARANTA KUMA: Kuma dai: Wata Katafariyar Gada da Gwamna Rochas ya gina ta rushe a birnin Owerri

Gwamnan ya kuma shawarci wadanda suka ribaci wannan tagomashi da yayi, inda ya neme su akan kauracewa duk wani nau'in laifi a lokuta na gaba da zai sanadiyar komawar su gidan Kaso.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamna Al-Makura zai gana da Fursunonin a ranar Juma'ar mai gabatowa domin danka su a hannun 'yan uwan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel