Da dumin sa: PDP ta maka APC da kasa a zaben maye gurbi a jihar Kaduna

Da dumin sa: PDP ta maka APC da kasa a zaben maye gurbi a jihar Kaduna

Mista Philip Gwada na jam’iyyar PDP ya lashe zaben maye gurbin karamar hukumar Jaba da aka sake yi a jihar Kaduna.

Da yake sanar da sakamakon zaben a garin Kwoi a yau, Alhamis, Baturen zabe, Grace Dorayo, ya bayyana cewar dan takarar PDP, Gwada, ya samu kuri’u 17,967 yayin da abokin takarar sa, Mista Benjamin Jok, ya samu kuri’u 7,401.

Doyaro ya bayyana zaben a matsayin mai tsafta tare da sanar da cewar ba a samu rikici ko rahotannin yin magudi a zaben ba. Kazalika ya bayyana cewar PDP ta lashe dukkan kujerun kansila 10 dake karamar hukumar.

Da dumin sa: PDP ta maka APC da kasa a zaben maye gurbi a jihar Kaduna

Da dumin sa: PDP ta maka APC da kasa a zaben maye gurbi a jihar Kaduna

A watan da ya gabata ne aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kaduna inda jam’iyyar PDP ta lashe guda 5, APC ta samu nasara a kananan hukumomi 12 yayin da wasu kananan hukumomin aka bayyana cewar sai an sake gudanar da zaben su.

PDP tayi nasara a kananan hukumomin; Jema’a, Zangon Kataf, Kachia, Sanga, da Kauru.

DUBA WANNAN: 12 ga watan Yuni: Yadda Buhari ya kawo karshen munafurci da makircin Obasanjo - Falana

Kamfanin dillanci labarai ya ce bai samu sakamakon kananan hukumomin Kagarko da Kajuru ba, yayin da ake cigaba da jiran sakamakon zaben karamar hukumar Kaduna ta kudu.

A yayin da jam’iyyar APC ta bayyana gamsuwar ta da sakamakon zaben kananan hukumomin, jam’iyyar PDP tayi korafin cewar an tafka magudi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel