Sabuwar Ranar Demokuradiyya: Wasu Shugabannin Najeriya sun yabawa Shugaba Buhari

Sabuwar Ranar Demokuradiyya: Wasu Shugabannin Najeriya sun yabawa Shugaba Buhari

Mun samu rahoton cewa wasu shugabannin kasar nan ta Najeriya sun yi yabo da jinjina ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da kaddamar da sabuwar ranar gudanar da murna da tunawa da Dimokuradiyya a Kasar nan.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaba Buhari ya kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokuradiyya a Kasar nan a madadin ranar 29 ga watan Mayu kamar yadda aka saba gudanar da murna a kasar nan.

Baya ga haka shugaba Buhari ya karrama Marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban Kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya watsar da sakamakon sa.

Shugaba Buhari yayin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Shugaba Buhari yayin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2015.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan rana ita ce ranar da ake rantsar da sabon shugaban kasa da yayi nasara yayin kammala zaben Dimokuradiyya na kasa bayan kowace shekara hudu a Najeriya.

A sanadiyar haka ya sanya wasu shugabannin Kasar suka yi jinjina da yabo ga shugaba Buhari sakamakon wannan namijin kokari da ya yi a lokacin gwamnatin sa.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta Cafke 'Yan Fashi da Makami 4 tare da Muggan Makamai a jihar Enugu

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Premium Times sun bayyana ire-iren shugabannin kasar nan da suka yabawa shugaba Buhari kamar haka; Gwamna Akinwunmi Ambode na Jihar Legas da Gwamna Muhammad Abdullahi Bindow na jihar Adamawa.

Sauran wadanda Shugaba Buhari ya cancanci yabon su sun hadar da; Gwamna rauf Aregbesola na jihar Osun, Tsohon shugaban Jam'iyyar PRP Alhaji Balarabe Musa, Tsohon Kwamishinan aikace-aiakace na jihar Enugu, Dakta Paul Okorie da kuma wani dan majlisar jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye.

Hakazalika wasu kungiyoyin kasar nan sun jinjinawa kwazon shugaba Buhari da suka hadar da; Kungiyar Ma'aikatan man fetur da makamashin Gas ta NUPENG da kuma Jam'iyyun Najeriya ta CNPP (Conference of Nigerian Political Parties).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel