Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ya kaure da hayaniya kan June 12

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ya kaure da hayaniya kan June 12

Zauren majalisar wakilai ya kaure da hayaniya yayinda mambobi suka ki aminta da kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Demokradiyya da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu yan majalisan sun goyi bayan hakan yayinda wasu suka bukaci shugaban kasa ya janye hukuncin.

Kakakin majalisa Yakubu Dogara na kokarin daidaita hayaniyan domin ci gaba da muhawaran.

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ya kaure da hayaniya kan June 12

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ya kaure da hayaniya kan June 12

Wasu daga cikin yan majalisan sun ja da karramawar da aka ba Moshood Abiola, mutumin da ya lashe zaben 12 ga Yuni na 1993 wanda sojoji suka soke.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisa sun sha da kyar lokacin zaben karamar hukuma a Kaduna (hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar kare muradun Yarbawa zalla ta Afenifere ta yabawa Buhari kan wannan mataki da ya dauka na girmama Abiola tare kuma da canja ranar dimokradiyya sai dai kuma kungiyar ta nuna shakku kan manufar siyasa da Buhari ke son cimma wa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel