An gano kwayar da tafi haukata matasa a jihar Kano

An gano kwayar da tafi haukata matasa a jihar Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa karin adadin mutane da ke fama da ciwon hauka na da alaka da shaye-shayen codeine a jihar

- Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin, Pharmacist Samaila Ciroma, Sakataren kwamitin masana kimiyyan magunguna na ma'aikatan lafiya a jihar

- Ciroma ya kuma ce kwamitinsa a shirye ta ke don yakar duk masu safara da ta'amuli da miyagun kwayoyi musamman codeina a jihar

A jiya ne gwamnatin Kano ta alakanta karuwar ciwon hauka da wasu ayyukan masha'a da ake aikatawa a jihar da amfani da magunguna masu dauke da sinadarin codeine da wasu muggan kwayoyin da matasa ke ta'ammuli da su.

Bincike: An gano kwayar da tafi haukata matasa a jihar Kano

Bincike: An gano kwayar da tafi haukata matasa a jihar Kano

KU KARANTA: Ranar 12 ga watan Yuni: Yadda IBB ya soke zaben shugaban kasa na MKO Abiola a shekarar 1993

A yayin da ya ke magana bayan an kai wata samame a wasu wuraren da ake sayar da codeine din ba bisa ka'ida ba, Sakataren kwamitin masana kimiyyan magunguna ta ma'aikatan lafiya na jihar, Pharmacist Samaila Ciroma ya ce kwamitinsa ta dau alwashin dakatar da amfani da codeine a jihar.

Ciroma ya kuma ce kwamitinsa a shirye ta ke don yakar duk masu safara da ta'amuli da miyagun kwayoyi musamman codeina a jihar. Ya ce ba za'a saurara wa duk wani kamfani magunguna ko dan kasuwa da aka samu yana cigaba da sayar da codeine a jihar.

Wannan matakan na zuwa ne baya gwamnatin tarayya ta kafa doka wadda ta haramta sarrafawa ko kuma shigo da magunguna masu dauke da codeine a Najeriya baki daya.

Gwamnatin har ila yau ta bayar da umurnin zagaya kasuwanni da kamfanoni don janye dukkan wasu magungunan masu dauke da sinadarin ta kodin kafin su shiga hannun al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel