Yan majalisa sun sha da kyar lokacin zaben karamar hukuma a Kaduna (hotuna)

Yan majalisa sun sha da kyar lokacin zaben karamar hukuma a Kaduna (hotuna)

Wasu yan majalisa biyu a jihar Kaduna da jami’in hukumar zabe mai zaman kanta sun sha da kyar a jiya a Kujama, karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.

Anyi zargin cewa an kama yan majalisan biyu ne suna satan kayayyakin zabe a satariyar majalisa dake Kujama.

Yan majalisan sune Abubakar Mohammed Mamadida Mark Yari.

Chikun ya kasance daya daga cikin jalisun da ba’a kammala zabe ba a zaben ranar 12 ga watan Mayu da aka yi sannan kuma an shirya zaben ne a jiya.

Yan majalisa sun sha da kyar lokacin zaben karamar hukuma a Kaduna

Yan majalisa sun sha da kyar lokacin zaben karamar hukuma a Kaduna

Anyi zargin cewa sun iso majalisar sakatariya tare da wani babban jami’in gwamnati, yan iska da kuma wasu jami’an tsaro.

Fusatattun masu zanga-zanga da suka iso sakatariyar basu yi masu ta dadi ba.

An rahoto cewa yan iskan da suka zo tare jami’in gwamnatin da yan majalisan sun tsere zuwa Kaduna da mashin din kuri’a kafin matasan sun iso, amma an lalata motocin Peugeot uku, ciki harda wanda ke dauke da kayayyakin zabe da suka bari.

Yan majalisa sun sha da kyar lokacin zaben karamar hukuma a Kaduna (hotuna)

Yan majalisa sun sha da kyar lokacin zaben karamar hukuma a Kaduna (hotuna)

Da kyar jami’an tsaro suka samu suka tserar day an majalisan daga hannun fusatattun matasan wanda suka yiwa majalisar kawanya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel