Kuma dai: Wata Katafariyar Gada da Gwamna Rochas ya gina ta rushe a birnin Owerri

Kuma dai: Wata Katafariyar Gada da Gwamna Rochas ya gina ta rushe a birnin Owerri

Mun samu rahoton cewa wata katafariyar Gada ta rushe dake harbar wasanni da nishadin yara da gwamnatin Rochas Okorocha ta gina a cibiyar Ikemba Ojukwu a birnin Owerri na jihar Imo.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito sun bayyana cewa, wannan tsautsayi ya afku ne a ranar Larabar da ta gabata sai dai an taki sa'a ba bu asarar rai ko guda ballantana ya kai ga rauni.

Legit.ng ta fahimci cewa wannan lamari ya janyo cecekuce da sukar gwamnatin jihar musamman iyaye da suka ziyarci wannan wuri tare da 'ya'yayen su a ranar 27 ga watan Mayu yayin tunawa da murnar ranar yara ta shekarar 2018.

Kuma dai: Wata Katafariyar Gada da Gwamna Rochas ya gina ta rushe a birnin Owerri

Kuma dai: Wata Katafariyar Gada da Gwamna Rochas ya gina ta rushe a birnin Owerri

'Yan Jarida na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya da suka ziyarci wannan wuri sun ruwaito cewa, tsautsayin ya afku ne a sakamakon ruwan sama mai karfi da ya sauka a daren ranar Talatar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Wani 'Barawon Babur ya gurfana Gaban Kuliya a Jihar Ekiti

Rahotanni sun bayyana cewa wannan Katafariyar Gada da gwamnatin jihar Imo tana daya daga cikin hanyoyin samar da kudaden shiga a fadin jihar musamman ta bangaren yawan bude idanu da shakatawa.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake sabunta mukaman wasu manyan Likitoci biyu na kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel