Tsohon gwamna Yero ya saki fursunoni 31 a jihar Kaduna

Tsohon gwamna Yero ya saki fursunoni 31 a jihar Kaduna

Bayan gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Dr Mukhtar Ramalan Yero da wasu hudu da hukumar EFCC tayi a gaban babban kotun tarayya a a ranar 31 ga watan Mayu akan kudin yakin neman zaben 2015, Yero ya biya taran wasu fursunoni talatin da daya.

An dai garkame fursunonin ne akan laifuka daban-daban da suka aikata a babban gidan yarin Kaduna ta tsakiya.

Wannan karamcin na daga cikin koyarwan annabi Muhammadu SAW taimakon mabukata da kuma yantasu musamman a watan Ramadana.

Fursunonin 31 sun kasance wadanda aka ba zabi na tara yayinda sauran suka kasance da zabi na tara da kuma diyya amma aka garkame su saboda basu da abun biya.

Mai girma, Ramalan Yero mutun ne mai alkhairi don haka yayi amfani da damar garkame shi da akayi a gidan yarin Kaduna a matsayin wani dama na yanta mutane 31 da aka riga aka daure.

Tsohon gwamna Yero ya saki fursunoni 31 a jihar Kaduna

Tsohon gwamna Yero ya saki fursunoni 31 a jihar Kaduna

Ya kuma kalubalanci fursunonin da su zamo masu da’a da kyawawan dabi’u tare da koyon darasi a zamansu na gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Sabuwar PDP na shirin tsinkewa daga APC a ranar 23 ga watan Yuni - Majiyoyi

Mutane 31 sun kasance mata da maza daga addinai daban-daban.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel