Fashin Offa: 'Yan siyasa ne basu so a gabatar da bincike akan Saraki

Fashin Offa: 'Yan siyasa ne basu so a gabatar da bincike akan Saraki

Wata kungiya ta yan asalin garin Offa, wadda shugaban matasan garin, Prince Femi Whyte, ya hada ta zargi yan siyasar jihar da bata binciken da 'yan sanda suke yi dangane da fashi da makamin da akayi a yankin har yayi sanadiyyar rasa rayuka 33

Fashin Offa: 'Yan siyasa sune suke bata mana aiki - Hukumar 'yan sanda

Fashin Offa: 'Yan siyasa sune suke bata mana aiki - Hukumar 'yan sanda

Wata kungiya ta yan asalin garin Offa, wadda shugaban matasan garin, Prince Femi Whyte, ya hada ta zargi yan siyasar jihar da bata binciken da 'yan sanda suke yi dangane da fashi da makamin da akayi a yankin har yayi sanadiyyar rasa rayuka 33.

Matasan sun dauki fostoci a yayin zanga zangar lumanar da sukayi a fadin garin, sunyi kira ga yan sanda dasu tabbatar da an gurfanar da yan fashin tare da masu taimaka musu a gaban shari'a.

DUBA WANNAN: Wasu marasa imani sun kashe ma'aikacin wutar lantarki da jifa da duwatsu

Mai magana da yawun kungiyar, Chief Muideen Babalola, yayi kira ga hukumar yan sandan dasu tabbatar da anyi adalci ga koma waye ke da sa hannu a lamarin.

Masu zanga zangar lumanar sun fara daga makarantar Firamare ta Iyeru Okin, suka kuma kare a Ijagbo, kusa da filin masallacin idi. Sun tsaida tattakin ne a fadar sarkin garin.

A fadar sarkin, daga cikin manyan fadar, Asalofa na Offa, Chief Isiaka Adebayo Shitu, wanda yayi jawabi a maimakon sarkin Offa, Oba Mufutau Gbadamosi wanda ya tafi umara kasar Saudiyya.

Shugaban yace, za a tabbatar abinda suke ma zanga zangar akai sannan za'a sanar da wadanda ya dace.

Amma a halin yanzu, sarkin Offa, Oba Mufutau Gbadamosi Esuwoye II, yace ayi binciken da ya dace ganin cewa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya dauki Offa a matsayin mahaifarshi.

A wata magana da babban sakataren shi yayi, Dr Tajudeen Oloyede, Oba Esuwoye yayi kira ga hukumar yan sandan da su sauke nauyin su kuma su cire son zuciya gurin yin bincike ballantana na fashi da makami.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel