Sama da mutane 1,000 sun canja sheka daga PDP zuwa APC

Sama da mutane 1,000 sun canja sheka daga PDP zuwa APC

Jam'iyyar APC ta garin Iwo, dake jihar Osun, ta karbi sama da mutum 1,000 wadanda suka canja sheka daga jam'iyyar PDP

Sama da mutane 1,000 sun canja sheka daga PDP zuwa APC

Sama da mutane 1,000 sun canja sheka daga PDP zuwa APC

Jam'iyyar APC ta garin Iwo, dake jihar Osun, ta karbi sama da mutum 1,000 wadanda suka canja sheka daga jam'iyyar PDP. Shugabannin jam'iyyar ta APC sune suka karbi masu canja shekar, a lokacin da suke gabatar da wani taro da wani shugaban gargajiya na yankin Iwo ya hada, Cif Diekola Ismail Adefowope, taron da aka gabatar a babban dakin taro na garin Iwo.

DUBA WANNAN: Wasu marasa imani sun kashe ma'aikacin wutar lantarki da jifa da duwatsu

Wani tsohon jigo a jam'iyyar PDP shine ya jagoranci kungiyar masu canja shekar, Mista Ajao Muritala Olaleye, yace sun yanke hukuncin barin jam'iyyar ne saboda jam'iyyar PDP ba ta da wani hadin kai, sannan kuma jam'iyyar tana yin abu kawai domin cigaban kanta bana al'umma ba. Taron wanda ya samu halartar mutane masu tarin yawa, wadanda suka hada manyan 'yan siyasa na yankin, shugabannin gargajiya, kungiyoyin siyasa, mawaka da kuma shugabannin dalibai.

A bayanin da yayi, gwamnan jihar ta Osun, Rauf Aregbesola ya jinjinawa Adefowope da kokarin da yayi, sannan kuma ya bada tabbacin cewar jam'iyyar zata kula da wadanda suka canja shekan kamar yanda ya kamata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel