Wasu marasa imani sun kashe ma'aikacin wutar lantarki da jifa da duwatsu

Wasu marasa imani sun kashe ma'aikacin wutar lantarki da jifa da duwatsu

Hukumar 'yan sanda sun kama wasu mutane mazauna garin Ota-Idiroko dake yankin Ota a cikin jihar Ogun, wadanda ake zargi da jifan wani ma'aikacin wutar lantarki na yankin jihar Enugu, mai suna Peter Ayole

Wasu marasa imani sun kashe ma'aikacin wutar lantarki da jifa da duwatsu

Wasu marasa imani sun kashe ma'aikacin wutar lantarki da jifa da duwatsu

Hukumar 'yan sanda sun kama wasu mutane mazauna garin Ota-Idiroko dake yankin Ota a cikin jihar Ogun, wadanda ake zargi da jifan wani ma'aikacin wutar lantarki na yankin jihar Enugu, mai suna Peter Ayole. Ayole mai shekaru 52 an tabbatar da cewar ma'aikacin wuta ne a garin Abakaliki, wanda suke da ofis a jihar Ebonyi.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi wa majalisa kunnen uwar shegu

Marigayin wanda ya dauki hutu, ya bukaci yaje yayi hutun daya dauka tare da iyalin sa a gidan sa dake garin Ota.

Majiyar mu Legit.ng ta samu labarin cewar musu ne ya barke a tsakanin marigayin da wasu makotan sa, a dalilin karar injin janarato, inda ya bukaci mutanen dasu taimaka su kashe injin janaraton, amma suka ki a karshe ma suka yi ta jifan shi har ya mutu.

Bazawarar matar shi, mai suna Oluwafunmilayo Ayole, ta yi bayanin cewar lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 23 ga watan Mayu, 2018.

Ta ce, "Muna tare dashi a gida da safe, sai yace bari yaje gidan mu da yake ginawa yaga yanda masu aiki suke aikin su. Ko minti 30 ba ayi ba da barin shi sai, sai na samu kiran waya inda ake gaya mini cewar maigidana ya mutu sanadiyyar jifan shi da wadannan mutanen suka yi.

"Na samu labarin da yazo wurin ya hadu da masu aikin, inda wani daga cikin masu aikin yake fada mishi cewar baza su iya yin aikin su da wannan karar injin janaraton ba, dama maigidan nawa yasha yi mini magana akan su, kuma shi abinda yake so shine su matsar da injin janaraton su zuwa wurin da ba zai damu mutane ba."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel