Majalisar dokoki ta karyata makircin tsige shugaba Buhari

Majalisar dokoki ta karyata makircin tsige shugaba Buhari

A ranar Laraba, 6 ga watan Yuni, majalisar dokokin kasar ta karyata batun cewa tana shirya makirci domin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake Magana a shirin Sunrise Daily a Channels TV, shugaban kwamitin shari’a na majalisa, Hon. Razak Atunwa yace an gudanar da taron hadin gwiwa na majalissun dokokin kasar ne domin yin sharhi kan al’amuran kasa da kuma amincewa akan wata maslaha.

Dan majalisan dake wakiltan mazabar Asa/Ilorin a jihar Kwara yace zaman ya shafi magance lamuran gwamnati ne da kuma lamuran da zasu karfafa damokradiya a Najeriya.

“Babu wanda ya ambaci wani abu game da tsige shugaban kasar,” inji shi.

Majalisar dokoki ta karyata makircin tsige shugaba Buhari

Majalisar dokoki ta karyata makircin tsige shugaba Buhari

Ya bayyana ikirarin cewa majalisar dokoki na son tsige shugaban kasar a matsayin “wanda babu kamshin gaskiya ko kadan.”

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari Kotu ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari

Yace majalisar dokoki zata aikata abunda kundin tsarin mulki ya bata karfin yi ne kadai, don tabbatar da cewar an samu tsaro na rayuka da dukiya, da kuma cire tsoro da barazana daga ko wani dan kasa.

Idan dai bazaku manta ba a ranar Talata ne aka yi zargin cewa majalisa tayi barazanar tsige shugaban kasa Buhari idan har bai cika wasu sharuda 12 da ta gindaya masa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel