Sabuwar PDP na shirin tsinkewa daga APC a ranar 23 ga watan Yuni - Majiyoyi

Sabuwar PDP na shirin tsinkewa daga APC a ranar 23 ga watan Yuni - Majiyoyi

Majiyoyi abun dogaro da dama sun bayyana cewa tsofin mambobin jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC a 2013 na shirin komawa wata jam’iyya a ranar 23 ga watan Yui, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyoyin, ranar 23 ga watan Yuni mai muhimmanci ce kamar yadda a ranar ne jam’iyya mai mulki zata gudanar da babban taron tan a zabar sabbin shugabanni.

Legit.ng ta tattaro cewa wani babban dan siyasa wanda ke da masaniyan abubuwan dake faruwa a APC yace mambobin kungiyar sabuwar PDP da Kawu Baraje ke jagoranta sun kammala shiri don barin APC.

Wata majiya wacce da masaniya game da lamarin tace mambobin sabuwar PDP sun yanke shawarar barin APC kamar yadda a bayyane yake cewar jam’iyya mai mulki bata dauki ko wani mataki ba don magance korafe-korafensu.

Sabuwar PDP na shirin tsinkewa daga APC a ranar 23 ga watan Yuni - Majiyoyi

Sabuwar PDP na shirin tsinkewa daga APC a ranar 23 ga watan Yuni - Majiyoyi

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokoki ta karyata makircin tsige shugaba Buhari

Da yake maida martini akan zargin da ake na ficewarsu, Baraje yace babu wani jawabi da sabuwar PDP ta saki game da wannan lamari.

Haka zalika, hadimar Rabiu Kwankwaso, Binta Spikin tace bata da masaniya kan cewa an sanya ranar 23 ga watan Yuni a matsayin ranar sauya shekar yan sabuwar PDP, haka ma ubangidanta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel