Karramawar da Buhari ya yiwa Abiola da lambar girma ta GCFR ya saba ka'ida - Belgore

Karramawar da Buhari ya yiwa Abiola da lambar girma ta GCFR ya saba ka'ida - Belgore

Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya Alfa Belgore ya ce karramawar da shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa marigayi MKO Abiola da lambar yabo mafi girma a Najeriya ta GCFR ya saba wa ka'ida.

A yammacin yau ne shugaba Buhari ya karrama marigayin da ya lashe zaben shekarar 1993 da lambar yabon bayan ya kuma canja ranar demokradiyya ta Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni wato ranar da aka fadi sakamakon zaben da Abiola ya lashe.

Alfa Belgore wanda ya rike mukamin Alkalin Alkalai daga 2006 zuwa 2007 ya ce ba dai-dai bane a karrama wanda suka mutu da lambar yabon na kasa balle ma wanda tafi kowanne daraja kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

"Ba'a haka, mutanen da ke raye kawai ake bawa irin wannan lambar yabon," inji Belgore.

"Abinda kawai za'a iya masa shine a rada sunansa a wasu wurare amma ba dai a bashi lambar yabon ba."

Karramawar da Buhari ya yiwa Abiola da lambar girma ta GCFR ya saba ka'ida - Belgore

Karramawar da Buhari ya yiwa Abiola da lambar girma ta GCFR ya saba ka'ida - Belgore

KU KARANTA: Mazauna wani kauye a Filato sunyi wa makiyaya mummunar ta'asa

Belgore kuma ya ce ba'a tuntube shi ba kafin a bayar da lambar yabon duk da cewa yana cikin kwamitin masu amincewa da bayar da lambar yabon.

Mista Belgore ya ce a karkashin dokar karramawa ta kasa ta 1963, dakarun soji ne kawai da sauran masu sanya kayan sarki za'a iya karamawa da irin wannan lambar yabon bayan sun mutu.

Canja ranar demokradiyar da shugaba Buhari ya yi ta janyo cece-kuce tsakanin yan Najeriya, magoya bayan Buhari na ganin cewa abu ne mai kyau sosai yayin da yan adawa kuma suna ganin dabara ce kawai na janyo hankalin yarabawa akayi don ganin zaben 2019 na matso

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel