Kotu ta hana Buhari ya fadi ko nawa ya kashe lokacin da ya yi jinya a Landan

Kotu ta hana Buhari ya fadi ko nawa ya kashe lokacin da ya yi jinya a Landan

Babbar kotu a babban birnin tarayya, Abuja ta yanke hukunci a game da wata shari'a dake gabanta da akar shigar game da kudaden da shugaba Buhari ya kashe a lokacin jinyar da yayi a Landan a cikin shekarar da ta gabata.

A cewar alkalin kotun, ba dole ba ne Shugaban mai shekara 75 ya bayyana yawan kudin da aka biya lokacin da ya yi jinya a Landan a bara.

Kotu ta hana Buhari ya fadi ko nawa ya kashe lokacin da ya yi jinya a Landan

Kotu ta hana Buhari ya fadi ko nawa ya kashe lokacin da ya yi jinya a Landan

KU KARANTA: EFCC ta kara kama hadimin Dasuki

Legit.ng dai ta samu cewa wata kungiyar farar hula mai rajin kare hakkin dan adam da kuma tabbatar da kafuwar demokradiyya da sahihin shugabanci tare da samar da ababen more rayuwa ce ta shigar da kara a gaban kotun. Tun farko dai kungiyar ta bukaci babban bankin kasar ne watau CBN da ya bayyana kudaden amma sai ya ki bayyanawa.

Mai sharia John Tsoho ya ce dokar 'yancin samun bayanai ba ta bada damar bada bayani ba a batutuwan da suka shafi fitar da bayani kan wani ba tare da amincewarsa ba, in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel