Da dumin sa: Jama'a ga sabuwar sanarwa daga hukumar hana cin hanci da rashawa, EFCC

Da dumin sa: Jama'a ga sabuwar sanarwa daga hukumar hana cin hanci da rashawa, EFCC

Shugaban babban ofishin shiyya na hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) dake garin Fatakwal na jihar Ribas, Nnaghe Itam ya gargadi al'ummar Najeriya da su bi a hankali da 'yan damfara.

Mista Nnaghe Itam ya bayyana cewar kiran ya zama dole ne ganin yadda wasu bata gari ke zuwa suna yin badda-kama suna yaudarar mutane musamman masu hannu-da-shuni cewar wai su za su samar masu da kwangila a ma'aikatar rayawa da cigaban yankin Neja Delta watau Niger Delta Development Commission (NDDC).

Da dumin sa: Jama'a ga sabuwar sanarwa daga hukumar hana cin hanci da rashawa, EFCC

Da dumin sa: Jama'a ga sabuwar sanarwa daga hukumar hana cin hanci da rashawa, EFCC

KU KARANTA: Za'a fara kamen masu shan shisha a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa shugaban ya bayar da wannan sanarwar ne a ranar Talatar da ta gabata a yayin da yake ganawa da manema labarai a dakin taro na hukumar a can garin na Fatakwal.

A wani labarin kuma, Fitacciyar kungiyar nan ta hadakar 'yan kabilar Yarbawa a Najeriya da aka fi sani da Oodua People’s Congress (OPC) a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana jin dadin ta tare da cikakken goyon bayan ta ga majalisar tarayyar Najeriya game da kudurin ta na tsige shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar mai suna Frederick Fasehun wanda kuma majiyar mu ta samu inda a ciki ya bayyana cewa hakan ya zama dole idan dai har ana son demokradiyyar mu ta dore.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel