Fashin Offa: An kara kama wasu yaran Saraki guda 2

Fashin Offa: An kara kama wasu yaran Saraki guda 2

- A yau ne hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa har yanzu tana cigaba da binciken Sanata Bukola Saraki

- Sannan hukumar ta bayar da sanarwar samun nasarar cafke biyu daga cikin mutum uku da ake zargin sunyi fashi a bankin Offa, wadanda suke da alaka da Saraki

Fashin Offa: An kara kama wasu yaran Saraki guda 2

Fashin Offa: An kara kama wasu yaran Saraki guda 2

A yau ne hukumar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa har yanzu tana cigaba da binciken Sanata Bukola Saraki, sannan sun samu nasarar cafke biyu daga cikin mutum uku da ake zargin sunyi fashi a bankin Offa wadanda suke da alaka da Sanata Bukola Saraki.

Yan sandan sun ce an samu nasarar cafke mutane biyun ne da taimakon shugaban tawagar tasu Ayoade Akinnibosun a yayin wani fareti da aka gudanar a 3 ga watan Yunin nan.

DUBA WANNAN: Yanzu - yanzu: Hukumar 'yan sanda tace har yanzu bata janye kiran da take yiwa Saraki ba

Wadanda aka kama din dai sun hada da Alhaji Kehinde Gobiri wanda akafi sani da Captain da Alhaji Oba Shuaib Olododo a.k. a. Jawando. Sai na ukun su wanda ake nema a halin yanzu Alhaji Dona. Alhaji Kehinde Gobiri mai shekaru 47 yayin da shi kuma Alhaji Oba Shuaib Olododo yake da shekaru 53.

A bayanin 'yan sandan wadanda ake zargin yan asalin garin Ilorin babban birnin jihar Kwara sun yarda da laifukan da ake tuhumar su wanda sukayi a jihar ta Kwara inda suka bayyana cewar tare suke aiki da Sanata Bukola Saraki a matsayin yan bangar siyasar sa.

"Har yanzu dai anaci gaba da bincike, idan muka kammala zamu mikasu gaban kotu" inji jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda ta kasa, Mista Moshood Jimoh.

Shugabannin tawagar su biyar da yan koransu 17 wadanda suka yarda da laifin su sun aikata laifin fashi da makami a garin Offa 5 ga watan Afrilu, Sunyi fashi da makami a wasu bankuna guda 6, sunkai hari hedkwatar yan sanda, sun kashe mutane 33 wanda ya hada da jami'an yan sanda 9.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel