Baraka ta kunno kai tsakanin kamfanin Facebook da Whatsapp

Baraka ta kunno kai tsakanin kamfanin Facebook da Whatsapp

- Wata Baraka ta kunno kai tsakanin shugabannin kamfanonin Facebook da na Whatsapp a kan batun saka talla

- Shugabannin kamfanonin biyu sun hau teburin naki a kan batun tallar dake neman jawo masu yin asarar makudan kudi da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan $1.3

- Facebook da Whatsapp na sahun gaba a tsakanin kamfanonin sada zumunta dake yanar gizo

Wata Baraka ta kunno kai tsakanin shugabannin kamfanonin Facebook da na Whatsapp a kan batun saka talla.

Shugabannin kamfanonin biyu sun hau teburin naki a kan batun tallar dake neman jawo masu yin asarar makudan kudi da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan $1.3.

Baraka ta kunno kai tsakanin kamfanin Facebook da Whatsapp

Baraka ta kunno kai tsakanin kamfanin Facebook da Whatsapp

Takaddama ta barke tsakanin su ne bayan kamfanin Whatsapp ya bayyana shirin fara saka talla a kan manhajar, yunkurin da kamfanin Facebook ke ganin bai kamata ba tunda ta hanyar talla ne kamfanin Facebook ke samun kudaden shiga.

DUBA WANNAN: Yadda na tsallake rijiya da baya yayin da aka kawo min harin bindiga - Ministan Buhari

Kamfanin Whatsapp ya bayyana cewar yana son fadada hanyoyin samun kudin shigowa domin a halin yanzu kamfanin ya dogara ne da kudin da kamfanin Facebook ke bas hi, hakan ya saka shugaban kamfanin ke ganin cewar akwai bukatar su ma su ke saka talla a manhajar su. Hakan ya kawo barkewar takaddama tsakanin kamfanonin biyu, kamar yadda VOA Hausa ta rawaito.

Facebook da Whatsapp na sahun gaba a tsakanin kamfanonin sada zumunta dake yanar gizo. Akwai biliyoyin masu amfani da manhajojin biyu a fadin duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel