Yanzu Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta canja ranar demokradiyya

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta canja ranar demokradiyya

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin sabuwar ranar bukin demokradiya a Najeriya.

Gwamnatin ta bayar da sanarwan ne a yau Laraba, inda ta ce anyi wannan canjin ne don yin karamci ga marigayi MKO Abiola wanda ya lashe zaben shugabancin kasa na 12 ga watan Yunin 1993.

Har ila yau, Gwamnatin tarayyan ta kuma sake karama marigayi Abiola da lambar yabo na Grand Commander of the Federal Republic (GCFR).

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta canja ranar demokradiya

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta canja ranar demokradiya

KU KARANTA: Dubi yadda jihohin Arewa ke kan gaba wajen adadin mutanen da za'a dauka aikin 'Dan sanda

'Yan Najeriya da dama sun dade suna ganin cewa ranar 12 ga wantan Yunin ne ranar da aka gudanar da zabe mafi sahihanci a tarihin Najeriya kuma ranar da tafi dacewa zama ranar murnar demokradiya fiye ma da 29 ga watan Mayu da ranar 1 ga watan Octoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel