Da Matsala: An sake lallasa Super Eagles a karo na biyu kafin fara gasar cin kofin Daniya

Da Matsala: An sake lallasa Super Eagles a karo na biyu kafin fara gasar cin kofin Daniya

- A wasan sada zumunci na karshe kafin fara gasar kofin Duniya an samu nasara akan Najeriya

- Dama kuma Super Eagles din tayi rashin nasara a wasanta da kasar Ingila da ci 2-1

- Wannan Kwallo da Tomas Kalas ya jefa ne ya maƙale a ragar Najeriya har aka tashi ba tare da ta farke ba

Ɗan wasan aro na Ƙungiyar Chelsea Tomáš Kalas ne ya zurawa kasar Jamhuriyar Czech ƙwallonta ɗaya tilo a ragar Najeriya a minti na 24 bayan fara wasa.

Najeriya dai na a rukuni na 'D' kuma zata buga wasanta na farko ne a gasar kofin Duniya da ƙasar Crotia a ƙasar Russia ranar 16 ga watan Yuli.

Da Matsala: An sake lallasa Super Eagles a karo na biyu kafin fara gasar cin kofin Daniya

Da Matsala: An sake lallasa Super Eagles a karo na biyu kafin fara gasar cin kofin Daniya

Wannan Kwallo da Tomas Kalas ya jefa ne ya maƙale a ragar Najeriya har aka tashi ba tare da ta farke ba, duk uwa da nuna salon kwarewa da takura da suka nuna musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

DUBA WANNAN: Wata kalma a cikin wasikar Buhari ta saka Sanatocin Najeriya kyalkyalewa da dariya

Akwai buƙatar Super Eagles ɗin su ƙara zage damtsensu mutuƙar suna son taka wani mataki a gasar kofin Duniyar da za'a fara nan da yan kwanaki kadan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel