Yadda na tsallake rijiya da baya bayan an kawo min harin bindiga – Ministan Buhari

Yadda na tsallake rijiya da baya bayan an kawo min harin bindiga – Ministan Buhari

- Ministan ma’adanai na kasa day a ajiye aiki a yau, Kayode Fayemi, ya fadi, cikin raha, cewar zai koyi yadda ake kaucewa harsashi

- Fayemi na wadannan kalamai ne dangane da harin bindiga da aka kai kan taron kaddamar da takarar sat a gwamna a jihar Ekiti

- A ranar juma’a ta makon jiya ne wani jami’in dan sanda ya yi harbi a wurin taron yakin neman zaben Fayemi a jihar Ekiti

Dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar APC, Kayode Fayemi, y ace zai koyi yadda ake kaucewa harsashi a wurin shugaba Buhari, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Yadda na tsallake rijiya da baya bayan an kawo min harin bindiga – Ministan Buhari

Kayode Fayemi

Fayemi ya bayyana hakan ne a yau, Laraba, cikin raha yayin bankwana da abokan aikin sa a majalisar zartarwa ta kasa bayan ya ajiye mukamin san a minister domin mayar da hankali wajen yakin neman zaben zama gwamnan jihar Ekiti.

DUBA WANNAN: Zan tabbatar an maka Oyegun a gidan yari bayan ya bar mulkin APC - Rochas

Da yake Magana a karo na farko bayan kai harin bindigar da wani jami’in dan sanda ya yi, Fayemi, y ace Allah ne kawai ya tserar da shi don kuwa da tuni ya mutu.

Gwaman y ace ya yi godiya ga ubangiji da harsashin bai same shi sannan kuma ba wanda ya mutu sakamakon harbin dad an sandan ya yi duk da wasu sun samu raunuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel