Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jimamin saukar Ministansa daga mukami

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jimamin saukar Ministansa daga mukami

- Da alama shugaba Buhari yayi babban rashi a cikin Gwamnatinsa

- Ministan Tama da Karafa Kayode Fayemi ne ya ajiye Mukaminsa domin tsayawa takarar Gwamna a zaben da za'ayi wata mai kamawa a jiharsa ta Ekiti

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa a yau Laraba yayin zaman Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) dangane da saukar da Ministan Tama da karafa Kayode Fayemi yayi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jimamin saukar Ministansa daga mukami

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jimamin saukar Ministansa daga mukami
Source: UGC

Shi dai Fayemi shi ne dan takarar jam’iyyar APC a zaben Gwamna da za’a gudanar wata mai zuwa a jihar Ekiti. Don haka ya sauka daga mukaminsa na Minista.

Yayin bankwana da Ministan a lokacin taron Muhammadu Buhari ya ce maye gurbin ba karamin wahala ba ne duba da yadda zaben 2019 yake kara karatowa, don haka grubin yana bukatar samun Mutum jajirtacce domin hana ‘yan fasa kwauri satar ma’adanan kasar nan.

Shugaban kasar ya ce “Muna yi maka fatan alheri, amma tabbas zai dauki lokaci kafin kafin a samu wani Ministan kamarka, musamman ganin mun tunkari zaben 2019. Amma ya zama tilas mu lalubo wanda zai iya aiki tukuru wajen ganin ya tabbatar da janyo hankalin masu jari da kuma lura da ma’adananmu”.

KU KARANTA: Rikicin Duniya: Wani Malami mai wa’azi ya damfari ‘Dan Canji N12m amma ambayar da shi beli a N5m

Muhammadu Buhari ya ce “Ina sane na kyale shi domin ya koma garinsa do muna fata ya ci zaben duba da irin cigaban da ya kawowa harkar Ma’adai wanda sanin kowa ne ba’a bawa harkar kulawa ba tun bayan da Turawan Mulkin Mallaka suka tafi, sha’awarsu ta koma kan Man Fetur".

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jimamin saukar Ministansa daga mukami

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jimamin saukar Ministansa daga mukami

A lokacin da muka nada shi mukamin abu na farko da ya fara yi shi ne; “Tabbatar da bin doka ga duk masu sana’ar hakar ma’adanai a kasar nan, zaku iya tuna yadda Mutane suke cikin mawuyacin hali a jihar Zamfara sakamakon yadda wasu suke cutar da su ba tare da hakkinsu ba. Ina fata zai samu nasara a zaben da za’ayi a jiharsa”.

Ana sa jawabin Fayemi godiya yayi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ba shi damar aiki tare da shi da kuma amince masa sauka daga mukaminsa don ya ja ya ceci jiharsa Ekiti. Sannan ya godewa abokanan aikinsa a Ma’aikatar sakamakon hadin kai da suka ba shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel