An kama wani mutum yayi wa 'yar shekara 9 fyade a jihar Sokoto

An kama wani mutum yayi wa 'yar shekara 9 fyade a jihar Sokoto

A jihar Sokoto wata babbar kotu ta daure wani mutum mai suna Muhammad Rilwanu mai shekaru 24 da laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 9 a duniya fyade

An kama wani mutum yayi wa 'yar shekara 9 fyade a jihar Sokoto

An kama wani mutum yayi wa 'yar shekara 9 fyade a jihar Sokoto

A jihar Sokoto wata babbar kotu ta daure wani mutum mai suna Muhammad Rilwanu mai shekaru 24 da laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 9 a duniya fyade. Wanda ake zargin, wanda yake zaune a yankin Gidanhaki a cikin jihar Sokoto, kotu tana tuhumar sa da laifin aikata fyade.

DUBA WANNAN: Sanata Stella Oduah ta canja sheka daga PDP zuwa APGA

Alkalin kotun, Mai shari'a Abubakar Adamu, ya bada umarnin tsare mai laifin a gidan kaso, inda yace kotu baza ta yanke hukunci akan laifin nasa ba a yanzu. Alkalin ya daga shari'ar zuwa ranar 21 ga wannan watan.

Mai kawo karar, Nasiru Auta, ya fadawa kotu cewar lamarin ya faru ne a ranar 10 ga watan Mayu a cikin shagon wanda ake tuhumar. A fadar shi yace, wanda ake zargin ya jawo yarinyar zuwa cikin shagon sa, inda ya yi mata fyade a cikin shagon.

Auta yace an sanarwa da hukumar tsaro ta Civil Defence Corps (NSCDC), dake jihar Sokoto, inda mahaifiyar yarinyar mai suna Aisha Ibrahim ta kai kara

Laifin ya sabawa sashi na 288 na dokar kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel