Gidan yari zaka wuce bayan ka sauka daga shugabancin APC – Gwamna Okorochas ga Oyegun

Gidan yari zaka wuce bayan ka sauka daga shugabancin APC – Gwamna Okorochas ga Oyegun

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce babu inda ya fi dacewa da shugaban jam’iyyar APC mai baring ado, Cif John Oyegun, da ya wuce gidan yari da zarar ya mika mulki ga sabon shugaban jam’iyyar da za a zaba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan Oyegun ya rantsar da sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar Imo, Hillary Eke, mutumin da basa ga maciji da gwamna Rochas.

Okorocha ya ce Oyegun ya rantsar da Eke duk da umarnin kotu na hana rantsar da duk wasu shugabanni da aka zaba bisa yanayi mai rudarwa.

Gidan yari zaka wuce bayan ka sauka daga shugabancin APC – Gwamna Okorochas ga Oyegun

Gwamna Okorochas ga Oyegun

Gwamnan ya zargi Oyegun da yunkurin gurgunta jam’iyyar APC bayan gaza cimma burin san a ganin ya dawwama a shugabancin jam’iyyar na kasa.

Yadda ya nace sai ya cigaba da shugabancin jam’iyyar APC ya isa mu gane irin hadamar da Oyegun yake da ita. Ba jam’iyyar ce a ran sa ba, bukatar kan say a fi bawa muhimmanci," a cewar Okorocha cikin jawabin da kakakin sa, Sam Onwuemeodo, ya raba ga manema labarai.

DUBA WANNAN: Kofa da Gudaji sun fada tsaka mai wuya a majalisa saboda soyayyar Buhari, an fara binciken su

Okorocha ya kara da cewar, shine ran APC a yankin kudu maso gabas na ‘yan kabilar Igbo tare da bayyana cewar yunkurin Oyegun na kassara jam’iyyar a yankin ba zai samu wuri ba saboda tsagin day a kirkira ba tare yake da jama’a ba.

Rochas y ace ba zai zuba ido wasu marasa kishin APC su rushe ginin da ya yiwa jam’iyyar a jihar Imo da yankin kudu maso gabas ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel