Yanzu-yanzu: Wasu sabbin yan fashi sun ambaci Saraki matsayin uban gidansu

Yanzu-yanzu: Wasu sabbin yan fashi sun ambaci Saraki matsayin uban gidansu

Kuma dai, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya kuma shiga tsaka mai wuya yayinda wasu sabbin yan fashin Offa sun ambaceshi a matsayin uban gidansu.

Hukumar yan sandan Najeriya tace har yanzu ana gudanar da bincike kan shugaban majalisan dattawan tun lokacin da yan fashin suka ambacesa ranan Laraba.

Kakakin hukumar yan sandan, Jimoh Moshood, yayinda hira da manema labarai a Abuja yace wasu sabbin yan fashi biyu da aka kama kwanakin nan sun sake ambatan sunan shugaban majalisan dattawa.

Yanzu-yanzu: Wasu sabbin yan fashi sun ambaci Saraki matsayin uban gidansu

Yanzu-yanzu: Wasu sabbin yan fashi sun ambaci Saraki matsayin uban gidansu

Hukumar yan sanda ta ce yan fashin sun yi bayanin cewa shugaban majalisa Bukola Saraki ne uban gidansu kuma sun rakashi fadar sarkin Offa domin jaje bayan fashin da ya faru a Offa.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa jami'an 'Yan Sandan Najeriya sun gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki ya hallara a gaban su kan wani fashi da aka yi kwanaki a Jihar Kwara domin ya wanke sa.

KU KARANTA: Ana tsananin fama da duhu a Garin Shugaban Kasa Buhari

Idan ba ku manta ba dai kwanaki ne aka yi wani mummunan fashi da makami a wani banki a Garin Offa da ke cikin Jihar Kwara. Ana zargin cewa akwai sa hannun Shugaban Majalisar Tarayyan a wajen wannan danyen aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel