Barazanar Banza ce Kawai - Matasan Jihar Edo ga Majalisar Dokoki ta Tarayya

Barazanar Banza ce Kawai - Matasan Jihar Edo ga Majalisar Dokoki ta Tarayya

Wata Kungiyar Matasa 'yan sa kai ta jihar Edo, ta yi gargadi ga Majalisar Dokoki ta tarayya akan ta daina yiwa shugaban Kasa Muhammadu Buhari barazanar tsige shi daga Karagar sa ta mulki domin cimma manufofi na soyuwar zukatan su.

Kungiyar ta EYVP (Edo Youth Volunteer for Progress) ta bayyana cewa barazanar banza ce kurum Majalisar ke yiwa Shugaba Buhari na tsige shi daga kan kujerar sa ta mulki domin kuwa Fankan-Fankan ba ta yi Kilishi.

Kamar yadda shafin Jaridar The Nation ya ruwaito, Kaungiyar ta kuma bayyana cewa ba bu jinkirin Kiranye da za ta yi akan wani dan Majalisar Jihar Edo da ya goyi bayan tumbuke shugaba Buhari daga Kujerar sa.

Shugaban wannan Kungiya, Mista Fred Okunmahie, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Babban Birni na Benin, inda yake cewa ko kadan 'yan Majalisar ba su damu da Kasar nan ba face son zuciya ta kawunan su da suka sanya a gaba.

Barazanar Banza ce Kawai - Matasan Jihar Edo ga Majalisar Dokoki ta Tarayya

Barazanar Banza ce Kawai - Matasan Jihar Edo ga Majalisar Dokoki ta Tarayya

Mista Okunmahie yake cewa, tuni lokaci ya riga da yi da ya kamata 'yan Majalisa na jam'iyyar APC mafi rinjaye a kasar nan su yi amfani da damar su wajen binne jam'iyyar adawa ta PDP dake shigo-shigo ba zurfin komawa karagar mulki a Najeriya.

Ya ci gaba da cewa, akwai ban dariya cikin sharuddan da 'yan Majalisar suka gindayawa shugaba Buhari na tsige shi daga kujerar mulki muddin bai cika su.

KARANTA KUMA: Mutane 189 sun yi nasarar Jarrabawar shiga Aikin 'Yan sanda a jihar Jigawa

A kalaman sa, "shin ko ta ya ya shugaba Buhari zai daina tozarta 'yan Majalisar da suka yiwa dokar kasa karan tsaye tare da saba ma ta?"

"Ko kadan ba su da hujja ta cewar shugaba Buhari ya na nuna wariya wajen fafata yakin sa da cin hanci da rashawa domin kurum mafi akasarin wadanda ke da Kashi a gindin su tawagar gwamnatin da ta shude ce."

"Saboda haka a mahangar mu barazanar Majalisar Dokoki ta Tarayya ba wata aba bace face Banza kuma ba ta haihuwar komai face Banza irin ta, domin kuwa ba bu wata Barazana da za ta daga hankalin Fadar shugaba Kasa Buhari a halin yanzu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel