Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa tarayya a yau Laraba, 6 ga watan Yuni2018 a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa, babban birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron majalisar sune ministan ayyuka, gidaje da wutan lantarki, Babatunde Raji Fashola, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, minstan Sufuri, Rorimi Amaechi, da karamin ministan wutan lantarki.

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Sauran sune mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, karamin minstan man fetur, Ibe Kachikwu, Shugaban ma'aikatan gwamnati, Winfred Oyo-Ita , ministan wasaani, Solomon Dalung da sauransu.

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Shi kuma ministan ma'adinai, John Kayode Fayemi ya halarci taron na karshe bayan ya yi murabus daga kujeran domin mayar da hankalin yakin neman zaben kujeran gwamnan jihar Ekiti wanda za'ayi a watn Yuli mai zuwa.

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC a yau

Majalisar zantarwa tarayya ta kunshi dukkan ministocin gwamnati, manyan masu baiwa shugaban kasa shawara, masu magana da yawunsa, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, shugaban ma’aikatan gwamnati, sakataren gwamnatin tarayya da kuma duk wani mai fada aji a fadar shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel