Buhari ma ya ci kudin makamai - Sule Lamido

Buhari ma ya ci kudin makamai - Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kum dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, Sule Lamido ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cin kudin makamai.

Lamido ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda yace tsohon mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya ba Buhari kyautar motoci masu sulke guda biyu bayan da Boko Haram suka kai masa hari a Kaduna.

Ya kara da cewa me ya sa Buhari ya gagara kama Jonathan, bayan duk wadanda ake tuhuma suna na da nasaba da tsohon shugaban kasar?

“Wai a ina Dasuki ya samu dala biliyan 2.5 da ya rarrabawa manyan mutane yayin da ake gab da zaben 2015, laifin da ya sa har yanzu yake daure a hannun hukumar DSS?

KU KARANTA KUMA: Tsige Buhari za mu yi tunda dai shi ba Allah bane – Jagaba

“Ga amsa, dukkaninsu sun samu kudaden ne daga babban bankin Najeriy, kuma tsohon shuhgaba Jonathan ne ya bada wannan umarni", cewar Lamido.

Daga karshe Sule yace: “Don haka tunda Alkali Binta Nyako ta yanke hukucin cewar bai kamata a kama duk wanda aka basu umarnin yin laifi ba, Gwmanatin Buhari ba zata iya kama Jonathan bane, ta gwada mu gani, da sai sama ta fado".

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labaranmu bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel