Allah ne ya amsa addu’ar mu, tilas a gurfanar da Saraki – Zanga – zanga ta barke a garin Offa

Allah ne ya amsa addu’ar mu, tilas a gurfanar da Saraki – Zanga – zanga ta barke a garin Offa

Wasu mazauna garin Offa a jihar Kwara, karkashin wata kungiya mai rajin kishin mutanen garin dake gida da ketare, sun bayyana cewar Allah ne ya amsa addu’ar su har ta kai ga hukumar ‘yan sanda ta gayyaci Saraki dangane da fashin ranar 5 ga watan Afrilu.

A wata zanga-zanga da mazauna garin Offa suka gudanar a jiya, Talata, inda suka yi tattaki daga wata makarantar firamare dake Okin Afrikan a Offa, su ka bi ta kan babban titin Ibrahim Taiwo sannan suka gudanar da addu’o’i a filin kasuwar Owode kafin su wuce zuwa fadar sarkin Offa, Olofa na Offa, Mufutau Gbadamosi, domin nuna goyon bayan su ga hukumar ‘yan sanda.

Allah ne ya amsa addu’ar mu, tilas a gurfanar da Saraki – Zanga – zanga ta barke a garin Offa

Bukola Saraki

A yayin zanga-zangar, mazauna garin na dauke da manyan takardu da aka yi tubutu daban-daban a jikin su dake nuna bukatar a tabbatar an yiwa mutanen da suka mutu yayin fashin adalci tare da bayyana bukatar a tuhumi Saraki.

DUB A WANNAN: Karanta cikakken jawabin 'yan fashin Offa da ya saka Saraki cikin tsaka mai wuya

A jawabin mai Magana da yawun kungiyar, Muyideen Babalola, ya bayyana cewar, yanzu fa an yi walkiya sun ga kowa tare da bayyana cewar gayyatar Saraki da hukumar ‘yan sanda tayi tamkar amsa addu’o’in su ne.

A ranar lahadi ne hukumar ‘yan sanda ta aikewa da Saraki sammacin ya bayyana a ofishin hukumar domin kare kan sa bayan ‘yan fashin garin Offa sun bayyana cewar su yaran sa ne kafin daga baya hukumar ta janye gayyatar tare da bukatar ya aike da jawabin sa a rubuce ga hukumar cikin sa’o’i 48.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel