Sakon majalisar dokoki ga Buhari a bayyane yake, suna iya fara shirin tsige shi - Idahosa

Sakon majalisar dokoki ga Buhari a bayyane yake, suna iya fara shirin tsige shi - Idahosa

West Idahosa, wani tsohon dan majalisar wakilai, yace sakon da majalisar dokoki ta aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a warware yake sannan kuma majalisar dattawa na iya ci gaba da shirin tsige shugaban kasar idan yaki basu hadin kai ga bukatarsu.

A ranar Talata, 5 ga watan Yuni majalisar dokokin kasar ta nuna rashin goyon bayanta ga sufeto janar na yan sanda Ibrahim Idris sannan kuma ta gargadi shugaba Buhari akan yadda bangaren dokoki ke muzanta tare da wulakanta yan siyasa masu adawa.

Idahosa a yayin hira da gidan talbiin din Channels TV shirin Politics Today yace maalisar dokoki na iya ci gaba da shirin tsige shugaba Buhari idan ya ki jin korafin ta.

Sakon majalisar dokoki ga Buhari a bayyane yake, suna iya fara shirin tsige shi - Idahosa

Sakon majalisar dokoki ga Buhari a bayyane yake, suna iya fara shirin tsige shi - Idahosa

A cewarsa an gabatar da maslaha da dama a baya ba tare da an dauki wani mataki akan su ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hukumar EFCC ta gurfanar da mataimakin gwamnan jihar Bauchi da wasu mutane 4 a gaban kotu (hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan majalisa mai wakiltan Kazaure, Muhammad Gudaji Kazaure yayi zargin cewa an fara tattara sa hannun sanatoci cikin sirri domin kulla makirci wajen tsige shugaban kasa Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel