Gwamnatin tarayya zata tura jami’an tsaro 2,000 na musamman jihar Zamfara

Gwamnatin tarayya zata tura jami’an tsaro 2,000 na musamman jihar Zamfara

A jiya, Talata ne, shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa, Ibrahim K. Idris, ya bayyana cewar nan bad a dadewa ba za a tura jami’ai 2,000 na musamman zuwa jihar Zamfara.

Idris ya fadi hakan ne a fadar gwamnatin tarayya bayan ganawar su da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ofishin sa.

A cewar Idris, za a tura jami’an tsaron na hadin gwuiwa zuwa jihar ta Zamfara cikin sati biyu masu zuwa tare da bayyana cewar taron su da shugaban kasa wata dam ace ta sanar das hi kalubalen tsaro da kasa ke fuskanta.

Gwamnatin tarayya zata tura jami’an tsaro 2,000 na musamman jihar Zamfara

Gwamnatin tarayya zata tura jami’an tsaro 2,000 na musamman jihar Zamfara

Da aka tambaye shi a kan kuri’ar rashin ingancin sad a majalisar kasa ta kada a kan sa, Idris ya bayyana cewar ba yanzu ne lokacin day a kamata a yi masa wannan tambayar nan sannan ya yi tafiyar sa abin sa.

DUBA WANNAN: Wata yarinya ta dawo gida shekaru 2 bayan mutuwar ta, an samu itace bayan tona kabarin ta

A wasu takarda da ya raba ga manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari, ministan tsaro, Mansur Dan Ali y ace majalisar tsaro ta damu matuka da yawaitar aiyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yamma musamman sata tare da yin garkuwa da mutane.

Ya bayyana aiyukan ta’addanci a kan babbar Abuja zuwa Kaduna a matsayin daya cikin abubuwan dake ciwa gwamnati tuwo a kwarya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel