Rikicin Duniya: Wani Malami mai wa’azi ya damfari ‘Dan Canji N12m amma ambayar da shi beli a N5m

Rikicin Duniya: Wani Malami mai wa’azi ya damfari ‘Dan Canji N12m amma ambayar da shi beli a N5m

- Malami ya shiga hannun jamia'an tsaro bisa damfarar wani makudan kudade

- Tuni har an gurfanar da shi gaban kuliya domin tabbatar da zargin da ake masa

- Sai dai shi ya ce sam bai aikata laifin komai ba

Wani Malamin Addinin Kirista mai shekaru 41 Segun Oyeniyi yana fuskantar shari'a a gaban wata Kotun Majistire dake zamanta a jihar Legas a dalilin tuhumarsa da damfarar wani ɗan Canji Kuɗi har Naira Miliyan N12m.

Amma sai dai shi Oyeniyi ya musanta laifukan da Kotun take tuhumarsa da su na haɗa baki wajen yin cuta da Damfara da kuma sata.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Sufeto Ben Ekundayo ya shaidawa Kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a watan Nuwambar shekarar da ta gabata (2017) a Legas Island.

Ya ce Malamin ya karɓi Kuɗi na dalar Amurka 102,000 daga ɗan canjin mai suna Ramadan Musa da zummar zai bayar da Kuɗin Naira kwatankwacin N3m.

Sai ya biya Naira Miliyan N20m amma yaƙi biyan cikon na N12m shi sai da aka takura masa sosai kafin ya biya.

KU KARANTA: Wasu 'Yan sanda 2 zasu fuskanci zazzafan hukunci bayan da aka kama su suna Caca

Wannan dai laifi ne da ya saɓawa sashi na 287 da 411 da 314 na kundin manyan laifuka na jihar ta Legas 2015.

Mutukar an tabbtar da aikata laifin dai sashi na 287 yayi tanadin shekaru Uku ne a magarkama yayin da sashi na 314 ya tanadi hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan Kaso, haka kuma sashi na 411 hunkuncin shekaru 2 ya tanada ga wanda ya aikata laifi irin wannan.

Yanzu haka dai bayan roƙon beli da ya shigar mai shari'a Magistrate Olumide Fusika ta amince da bayar da Malamin beli amma bisa sharaɗin Naira Miliyan N5m da kuma masu tsaya masa Mutum biyu da zasu iya biya.

Daga nan kuma ta dage Ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Yuni domin cigaba da shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel